Iraqi-Amurka

Ganawar Kerry da shugabannin Kurdawa a Iraqi

Sakataren harkokkin wajen Amurka John Kerry.
Sakataren harkokkin wajen Amurka John Kerry. Reuters

Sakataren harakokin wajen kasar Amurka, John Kerry, ya kai ziyara a yankin Kurdawan kasar Iraqi domin tattaunawa da shugabanninta kan yadda za a shawo kan rkicin kasar. Wanan ziyara na zuwa a dai-dai lokacin da Iraqi ke cigaba da fuskantar hare hare daga bangaren mayakan Sunni. 

Talla

Ganin cewa Kerry ya nisanta Amurka da rikicin Iraqi a baya, domin a cewarsa rikicin na cikin gida ne, inda ya kara da cewa gwamnatin Iraqi ta yi sakaci wajen daukan matakin gaggawa da zai dakile rikicin.

Kerry ya kuma sanar da cewa Amurka, za ta bayar da gudunmuwa na musaman wajen yakar mayakan Sunni dake cigaba da sa kai zuwa Bagadaza babban birni kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.