Iraqi-Amurka

Amurka ta fara tura dakarunta zuwa Iraqi

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing

Kasar Amurka ta fara tura dakarunta kusan 300 zuwa kasar Iraqi domin taimakawa dakarun Iraqi wajen ganin an shawo kan rikicin da aksar ke fama da shi. Sai dai ma’aikataron tsaron kasar ta Amurkata ce sojojin ba za su yi yaki kai tsaye da mayakan ba, sai dai su baiwa dakarun Iraqi shawara. 

Talla

Rahotanni sun ce yanzu haka kusan sojojin da shugaba Barack Obama ya tayin aikawa na birnin Bagadaza.

Sakataren harkokin wajen kasar Amurka, John Kerry ya yi kira ga daukai al’umar kasar da su hada kansu don ceto kasar daga daidaicewa

Kerry ya yi kiran ne yayin da ya kai ziyara kasar ta Iraqi inda ya gana da bangaren Kurdawa.

Sai dai tsohon mataimakain shugaban Amurka, Dick Cheney day a kitsa mamaye Iraqi a shekarar 2003, ya soki matakin da kasar ke dauka, inda yake cewa ya saba abinda ya dace.

Cheney wanda ya kare matakin da suka dauka na mamaye Iraqi, y ace bashi da wata nadama ko kadan kan abinda suka yi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.