Amurka

Shan Barasa na kisan Al’umma

Kwalaben giya a kasar Belerus
Kwalaben giya a kasar Belerus telegraf.by

Wani bincike da aka gudanar a Amurka ya nuna cewar yawan shan barasa fiye da kima, na zaman sanadin mutuwar mutum 1 cikin kawane 10 a kasar. Binciken da Cibiyar kariya da hana yaduwar Cutuka ta kasar Amurka ta gudanar, ya nuna cewar duk wadannan mace macen da ake samu a kasar na faruwa ne sakamakon hatsari da masu shan Barasa kan yi bayan sun bugu, ko kuma kamuwa da matsananciyar rashin lafiya.

Talla

Binciken cibiyar yace a duk shekara Amurka na yin hasarar kudi dala Biliyan dari biyu da ashirin da hudu daga irin ta’adin da shan barasan ke haifarwa.

Akalla dai mutane Dubu Tamanin da takwas ne ke mutuwa a Amurka kowace shekara sakamakon shan Barasa kuma Kashi 10 na masu mutuwar ‘Yan shekaru 20 ne zuwa 64.

Binciken kuma ya nuna cewar Maza sun fi Mutuwa akan shan Barasa a Amurka bisa ga Mata domin kashi 70 na masu mutuwar duka Maza ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.