Argentina

Za a gurfanar da mataimakin shugaban Argentina a gaban kotu

Mataimakin shugaban kasar Argentina Amado Boudou
Mataimakin shugaban kasar Argentina Amado Boudou Wikimedia Commons

Wata kotun kasar Argentina ta rubuta takarda caji kan mataimakn shugaban kasar Amado Boudou, da ake zargi da yin sama da fadi da kudaden jama’a, a lokacin yana rike da mukamin ministan kudin kasar. Wata majiya daga kotun ta tabbatar da hakan, sai dai a halin yanzu mataimamin shugaban na kasar Cuba, kuma ana fatan zai koma Argentina a cikin mako mai zuwa.Amado Boudou ne mataimakin shugaban kasar na farko, da aka taba yiwa irin wannan zargin a lokacin da yake kan mukamin shi.