Kwallon kafa

Mutane 2 sun mutu sakamakon wasannin zagaye na 2 a gasar cin kofin duniya

Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafan kasar Brazil
Wasu magoya bayan kungiyar kwallon kafan kasar Brazil Reuters/Arnd Wiegmann

Wani dan kasar Brazil mai shekaru 69 ya mutu sakamakon bugun zuciya, a lokacin da ake bugun daga kai sai mai tsaron gida, yayin wasan da aka yi taskanin Brazil din da Chile.Mutumin mai fama da ciwon suga, da ke kallon wasan a wata mashaya, yace baya jin dadi inda kuma aka garzaya dashi asibiti, kafin daga bisani ya mutu.Kafafen yada labarum kasar ta Brazil sun ce sai da aka yiwa fiya da mutane 100 magani a asibitoci, a lokacin wasan na jiya. Ita ma wata mace ta mutu, a sakamakon harsashi da ya subuce, ya same ta a lokacin da ake murnar samun nasarar da kasar Colombia tayi a zagaye na 2, na gasar cin kofin dunityan.Hukumomin kasar ta Colombia sun ce bayan da Colombiya ta sami nasara kan Uruguay ci 2-0, sai wani dan kasar ya harba bindiga sama saboda murna, amma sai harsashin ya sami wata mace ya kashe ta, wani mutumin kuma ya sami rauni a garin Bosa, da ke kudancin birnin Bogota.Ko a lokacin da Colombia ta sami nasara a kan Girka a wasanta na baya, sai da wasu ‘yan kasar su 9 suka mutu sakamakon shagulgulan da aka yi a wancan lokacin.