Iraq-Rasha

Rasha ta aikawa Iraqi da jiragen yaki

Dakarun Rasha suna tura jirgin Yakin kasar Sukhoi SU-25 a lokacin da ya isa sansanin Sojin Iraqi a al muthanna
Dakarun Rasha suna tura jirgin Yakin kasar Sukhoi SU-25 a lokacin da ya isa sansanin Sojin Iraqi a al muthanna (©Reuters)

Dakarun Iraqi na ci gaba da gwabza fada da Mayakan Sunni a garin Tikrit cibiyar Saddam Hussain, a yayin da kasar Rasha ta aikawa kasar da Jiragen yaki domin fatattakar Mayakan da suka karbe ikon wasu biranen kasar. Rahotanni sun ce dakarun Iraqi sun yi wa Mayakan luguden wuta ta jiragen sama, a yayin da suke ci gaba da kutsawa domin kwaton garin Tikrit da ya fada ikon gungun Mayakan na Sunni.

Talla

Manyan Kasashen duniya sun yi kira ga shugabannin Iraqi su gaggauta kafa gwamnatin Hadaka domin kawo karshen rikicin kasar da ya shafi banbancin akida tsakanin mabiya Sunni da Shi’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.