Pakistan

Pakistan ta kaddamar da sabbin hare hare a kan ‘yan Taliban

Wasu jiragen yakin Pakistan a lokacin da suke kai harin kan 'yan kungiyar Taliban
Wasu jiragen yakin Pakistan a lokacin da suke kai harin kan 'yan kungiyar Taliban Shia International News Association

Dakarun gwamnatin Pakistan sun kaddamar da sabon farmaki kan mayakan kungiyar Taliban a cikin lardin Waziristan a yau litinin.

Talla

Daruruwan sojojin kasar ne suka yi wa birnin Miranshah wanda shi ne gari mafi girma a lardin na Waziristan kawanya.

Garin na Waziristan, ya kasance yankin da ‘yan Taliban da kuma Alqa’ida ke amfani da shi domin gudanar da ayyukansu a cikin kasashen Pakistan da kuma Afghanistan.

Fadar Washington ta jima tana nuna matsinlamba kan kasar ta Pakistan da ta da
uki mataki kan ‘yan ta’adda dake mamaye da yankin na Waziristan.

“Ana amfani da tankunan yaki ne domin kaiwa ga mayakan.” Inji wani jami’in tsaron kasar ta Pakistan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.