Bosnia

Wani mutumin Bosnia ya je Makka a kafa

Senad Hadzic, a loakcin da yake takawa daga Bosnia zuwa Makka
Senad Hadzic, a loakcin da yake takawa daga Bosnia zuwa Makka

Wani Musulmin kasar Bosniya ya taka da kafa zuwa kasar Saudi Arabiya inda ya kwashe tsawon kilomita 5,700 domin ya gudanar da aikin Hajji. 

Talla

Mutumin ya shaidawa Kamfanin dillancin labarai na AFP cewar ya fara tafiyar ne a watan Disambar 2011 ya kuma isa kasar Saudi Arebiya ranar Asabar data gabata.

Senad Hadzic mai shekaru 47 ya ratsa kasashe bakwai ne ciki kuwa hadda kasashen da ake fama da yaki.

Hadzic ya ratsa cikin kasashe irinsu Serbia da Bulgaria da Turkiyya da Siriya da Jordan sannan ya ya fada Saudi Arabiya, duka kuma dauke da Jaka mai nauyin Kilogram 20 a bayansa.

Ya kara shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar ya ratsa kasar Siriya inda ake Yaki a tafiyar Kilomita 500 a cikin kwanaki 11, bayan da ya ratsa yanayi mai tsananin sanyi a Bulgariya da kuma mai tsananin zafi a Jordan.

Ya shiga birnin Damascus da Aleppon kasar Siriya, inda ya ratsa ta wuraren da ‘yantawaye ke rike da su da kuma wuraren da Sojin gwamnati ke rike da su, amma ko sau daya ba’a tsare shi ba.

Wannan tafiyar Hajjin da ya ce ya yi ne domin sauke farali, kasantuwar Hajji na daga cikin shikashikan Musulunci, ya kuma sadaukar da shi ne ga Iyayensa.

 

 

 

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.