Falasdinawa

Abbas ya nemi Isra’ila ta yi Allah wadai da kisan matashin Bafalasdine

Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas
Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas REUTERS/Mohamad Torokman

Shugaban Falasdinawa, Mahmud Abbas ya yi kira ga hukumomin Isra’ila, da su yi Allah wadai da kashe wani matashi Bafalasdine da aka yi a Jerusalem.

Talla

Rundunar ‘yan sandan Isra’ila ta tabbatar da tsintar wata gawar wani matashi a wani daji dake yammacin Jerusalem.

“Shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas, ya nemi Fira Ministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da ya yi Allah wadai da sace tare da kisan Mohammed Abu Khder, kamar yadda muka yi kan kisan matasan Isra’ila da aka yi.” Wata sanarwa da shugaba Abbas ya fitar ta ce.

Da yawa dai na kallon kisan wannan matashi na Falasdinawa, daukan fansa ne kan matasan Isra’ila guda uku da aka sace aka kuma kashe a ‘yan kwanakin nan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.