Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila da Hamas sun gargadi juna

Jami'an tsaron Isra'ila suna kwashe wani makamin Roka da aka harbo daga Gaza.
Jami'an tsaron Isra'ila suna kwashe wani makamin Roka da aka harbo daga Gaza. REUTERS/Amir Cohen

Isra’ila ta yi gargadin ci gaba da kai munanan hare-hare a yankin Gaza, matukar gwamnatin Hamas ba ta dauki matakan da suka wajaba domin hana kai wa Yahudawa hari ba. Yayin da kuma bangaren Hamas ke yin gargadi ga Isra’ila ta daina kai hare hare ta sama a zirin Gaza.

Talla

Yanzu haka Isra’ila ta tura Karin sojoji zuwa kusa da iyakarta da yankin Gaza, bayan da sojan saman kasar suka yi ruwa bama-bamai akan wasu yankuna bayan kisan da aka yi wa wasu yahudawa uku da kuma daukar fansar da yahudawan suka yi akan wani bafalasdine ta hanyar kashe shi.

Rundunar Sojin Isra’ila tace a shirye ta ke ta mayar da martani idan har Hamas na kai wa Yahudawa hare hare. Yayin da bangaren Hamas ke yin gargadi ga Isra’ila ta daina kai hare hare ta sama a zirin Gaza.

Wannan musayar kalamaun dai na zuwa ne bayan an yi arangama tsakanin Falasdinawa da ‘Yan sandan Isra’ila a rana ta biyu da aka kwashe ana zanga-zangar adawa da kisan matashin Bafalasine Mohammed Abu Khuder.

Yawancin Falasdinawa dai sun yi imanin an kashe matashin ne domin mayar da martani ga kisan Matasan Yahudawa guda uku da aka tsinci gawarsu bayan an sace su.

A yau juma’a ne ake sa ran za’a yi Jana’izar matashin.

Tun sace matasan yahudawan guda uku, Isra’ila ke sukar Hamas, yayin da Hamas kuma ta daura alhakin kisan matashin Bafalasdinen ga Isra’ila, al’amarin da ke kara hura wutar rikici a gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.