Amurka-Canada

Guguwar Arthur ta nufi Canada

Hoton Guguwar Artuhur da ta shafi yankunan kasar Amurka da Canada
Hoton Guguwar Artuhur da ta shafi yankunan kasar Amurka da Canada REUTERS/NASA/Handout via Reuters

Guguwar Arthur ta nufi yankin arewa maso gabacin Amurka zuwa wani yanki na kasar Canada amma ba tare da haifar da wani munmunan ta’adi ba, amma guguwar ta jefa Miliyoyan mutane cikin fargaba a daidai lokacin da Amurkawa ke gudanar da bikin ranar samun ‘Yanci.

Talla

Guguwar da aka bayyana ba ta kai girman guguwar Hurricane ba amma ta haifar da katsewar wutar lantarki a yankunan Nova Scotia da Halifax a kasar Canada.

Tun a ranar alhamis ne Guguwar Arthur, ta isa gabar jihar Carolina ta Arewa da ke kasar Amurka.

Hukumar hasashen yanayi ta Amurka, ta ce guguwar wadda za ta shafi yankuna da dama da ke gabashin kasar, ta kasance mai karfi, domin kuwa tana tafiyar kilomita 160 a cikin awa daya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.