Mu Zagaya Duniya

Sarkozy a hannun 'yan sanda

Sauti 21:01
Sarkozy na zantawa da wata tashar talabijin.
Sarkozy na zantawa da wata tashar talabijin. Screen capture/TF1

 A cikin shirin Mu Zagaya Duniya na wannan mako, Abdoulkarim Ibrahim Shikal ya tabo batutuwa da dama da suka fi daukar hankulan jama'ar duniya a makon da ya gabata, da suka hada da tsare tsohon shugaban Faransa Nicolas Sarkozy a hannun 'yan sanda, sanar da Daular Musulunci da mayakan jihadi suka yi a Iraki, yiyuwar kasa gudanar da zabe a tarayyar Najeriya da kuma yadda 'yan kasuwar Jamhuriyar Nijar ke neman gwamnatin kasar ta samar da dokoki da za su ba su kariya daga mamayar kamfanonin ketare.