Fadar Vatican

Brazil 2014: Fadar Vatican ta yi kiran a tsagaita wuta

Fafaroma Francis yana diba lokaci a agogonsa a lokacin zai gabatar da jawabi ga dimbim mabiya darikar Katolika a kasar Italiya
Fafaroma Francis yana diba lokaci a agogonsa a lokacin zai gabatar da jawabi ga dimbim mabiya darikar Katolika a kasar Italiya REUTERS/Max Rossi

Fadar Vatican ta Fafaroma a yau Juma’a ta yi kiran bangarorin da ke rikici a sassan kasashen duniya su tsagaita wuta a ranar Lahadi,  ranar da za’a buga wasan karshe a gasar cin kofin duniya da ake gudanarwa a Brazil. Wannan kiran na Vatican na zuwa ne a yayin da rikicin Gaza ke kazancewa da kashe-kashe a Ukraine.

Talla

Fadar Vatican ta bukaci a ware Minti guda a wasannin karshe na gasar cin kofin duniya domin Juyayin wadanda suka mutu a tashe tashen hankulan da ake samu a kasashen duniya.

A filin wasa na Maracana ne a birnin Rio de Janeiro Jamus da Argentina zasu buga wasan karshe a Brazil. Amma Zuwa yanzu babu wata sanarwa daga FIFA game da wannan kiran na Fadar Vatican.

Fafaroma Francis wanda dan asalin kasar Argentina ne ana sa ran zasu kalli wasan karshe ne tare da Fafaroma Benedict mai murabus wanda dan asalin kasar Jamus ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.