Isra'ila-Falesdinawa

Mutanen Gaza sun kauracewa gidajensu

Falasdinawa suna yin hijira daga gidajensu saboda hare haren da Isra'ila ke kai wa Gaza
Falasdinawa suna yin hijira daga gidajensu saboda hare haren da Isra'ila ke kai wa Gaza REUTERS/Ahmed Zakot

Adadin Falasdinawa 166 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa a zirin Gaza tsawon kwanaki shida ba kyafkyaftawa. Isra’ila ta yi kira ga Falasdinawa su kauracewa gidajensu, domin zata ci gaba da kai hare hare a Gaza.

Talla

Zuwa yanzu babu wani Bayahuden Isra’ila da aka ruwaito ya mutu a hare haren rokoki sama da 630 da ake harbawa wa zuwa Isra’ila daga yankunan Falasdinawa.

Dukkanin bangarorin biyu dai sun yi watsi da kiran tsagaita wuta da kasashen duniya ke yi.

Zuwa yanzu Falasdinawa sama da 1,000 ne suka jikkata a hare hare ta sama da Isra’ila ke kai wa a Gaza.

Tun a ranar Talata ne Isra’ila ta kaddamar da hare hare a Gaza.

Ana sa ran a yau Lahadi manyan kasashen duniya Birtaniya da Faransa da Jamus da Amurka zasu tattauna batun rikicin Isra’ila da Falasdinawa a Vienna bayan sun kammala tattauna batun Nukiliya tare da Iran.

Tuni Faransa ta yi kira ga bangarorin biyu su tsagaita wuta don kaucewa ballewar yaki a gabas ta tsakiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.