Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila da Hamas sun amince su tsagaita wuta

Wani Sansani da Isra'ila ke kai hare hare zuwa Gaza
Wani Sansani da Isra'ila ke kai hare hare zuwa Gaza REUTERS/Baz Ratner

Kasar Israila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa sun amince da bukatar tsagaita wuta da Majalisar Dinkin Duniya ta bukata na sa’oi biyar don bayar da damar kai kayan agaji, bayan shafe kwanaki 10 suna kai wa juna hare hare. 

Talla

Bangarorin biyu duk sun sanar da dakatar da hare haren da suke kai wa juna a yarjejeniyar ta sa’o;’I biyar, amma rahotanni sun ce da safiyar Alhamis Isra’ila ta ci gaba da kai hare hare a rana ta 10 da ta ke kai wa Falasdinawa hari a Gaza.

Falasdinawa kimanin 226 suka mutu a hare haren Isra’ila tare da jikkata 1,678 a Gaza, yawancinsu fararen hula.

Tun a ranar Takwas ga wata ne bangarorin biyu suka fara ruwan wuta a tsakaninsu, yayin da Falasdinawa ke amfani da makamin roka, ita kuwa Isra’ila tana amfani da jiragen sama da na ruwa wajen luguden wuta a Gaza.

Jami’an tsaron Isra’ila sun ce Hamas ta cilla rokoki 1,200 zuwa Isra’ila amma mutum guda ne aka ruwaito ya mutu, a ranar Talata.

Kungiyar Hamas ta bukaci wasu sauye sauye cikin yarjejeniyar zaman lafiya tsakaninta da Isra’ila da kasar Masar ta rubuta don kawo karshen tashin hankalin da ake ci gaba da yi tsakanin bangarorin biyu.

Mataimakin shugaban kungiyar Mussa Abu Marzuq wanda ya gana da wakilan gwamnatin Masar ne ya bukaci yin sauyin inji Azzam al ahmad wani jami’in shugaba Mahmud Abbas.

Sauyin da Hamas ke bukata sun hada da sanya yarjejeniyar shekarar 2012 na tsallaka iyakokin Isra’ila da kuma ‘yancin kamun kifi na mita 12 a cikin teku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.