Isa ga babban shafi
Libya-Amurka

Amurka ta rufe ofishin jekadancinta a Libya

Hayaki ya turmuke sama a Tashar jirgi a birnin Tripoli na Libya
Hayaki ya turmuke sama a Tashar jirgi a birnin Tripoli na Libya REUTERS/ Hani Amara
Zubin rubutu: Awwal Ahmad Janyau
Minti 2

Kasar Amurka ta rufe ofishin jekadancinta a birnin Tripoli tare da kwashe Jami’an diflomasiyarta daga kasar Libya saboda kazancewar rikici tsakanin mayakan sa-kai guda biyu da ke fada da juna a kasar.

Talla

Jami’an Amurka da dama ne aka tsallaka da su zuwa kasar Tunisia saboda rikicin kasar. Tuni gwamnatin Libya ta yi gargadin cewa Mayakan da ke rikici da juna na son ruguza kasar.

A cikin wata sanarwa daga Kakakin gwamnatin Amurka Marie Harf, ta yi gargadi ga Amurkawa su kaurace shiga kasar Libya tare da kira ga dukkanin Amurkawan da ke cikin kasar su fice.

A jiya Juma’a an samu barkewar wani sabon rikici tsakanin mayakan da ke fafatikar karbe ikon tashar jirgin sama na birnin Tripoli, bayan sun kwashe kwanaki suna kai wa juna hare hare da makaman rokoki.

Tun kawar da gwamnatin Kanal Gaddafi a 2011, shugabannin libya sun kasa tabbatar da tsaro a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.