Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila da Hamas sun ki tsagaita wuta

Hare haren Isra'ila a yankin Gaza
Hare haren Isra'ila a yankin Gaza REUTERS/Suhaib Salem

Isra’ila da Hamas sun ci gaba da kai wa juna hare hare, duk da sanarwar tsagaita wuta ta sa’o’I 24 da kungiyar Hamas ta bayyana. Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya amince ya yi kira ga bangarorin biyu su gaggauta tsagaita wuta domin dalilai na Jin kai, bayan mambobin kwamitin sun gudanar da wani taron gaggawa a daren jiya Lahadi.

Talla

Rikicin Gaza dai ya lukume rayukan Falasdinawa sama da 1,000 a kwanaki 20 da aka shafe Isra’ila na kai farmaki a Gaza, yayin da kuma aka kashe Sojin Isra’ila 43.

Firaministan Isra’ila Benyamin Natanyahu yace zasu ci gaba da kai hare hare domin kare kansu daga hare haren rokoki da Hamas ke cilla zuwa yankunan Isra’ila.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.