Isra'ila-Falesdinu

MDD tace Falasdinawa suna cikin wani mummunan hali

Wasu Palasdinawa 'yan gudun hijira
Wasu Palasdinawa 'yan gudun hijira REUTERS/Mohammed Salem

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta shaida wa kwamitin tsaron majalisar cewa Palasdinawa suna cikin halin tsaka mai wuya. Zuwa yanzu dubun dubatar Palasdinawa da suka tsere daga gidajensu, suna samun mafaka a wani ginin MDD.Cikin wani jawabin daya yi cikin kausasan kalamai, shugaban hukumar kula da Palesdinawa ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, Philippe Krahenbuhl ya shaida wa kwamitin tsaron majalisar cewa, cin zarafin da ake wa Palasdinawan ya kai kurewa.Krahenbuhl dake jawabi a gaban kwamitin tsaron mai Membobi 15, yace Palasdinawa 220,000 da ke samun mafaka a ginin majalisar Dinkin Duniya sun ninka abinda aka samu a rikicin yankin Gaza na shekarar 2008 zuwa 2009 har sau hudu.Kwamitin ‘yan gudun hijiran ya nemi kasshen duniya su dauki matakan da suka dace, don kawo karshen lamarin, da yace ya zarta tunanin dan AdamWakilin Palasdinawa a MDD Riyad Mansour yayi kira ga kwamitin tsaron, daya dauki tsauraran matakai don kawo karshen rikicin, tare da umartar Isra’ila ta fice daga yankunan Palasdinawa.