Isra'ila-Falesdinawa

Gaza: An sake kai mummunan hari a wata Makaranta

Wani Bafalasdine a kusa da Masallacin da aka tarwatsa dauke da wasu da kayansa da ya tsira da su a gidansa  a Khuzaa da ke kudancin Zirin Gaza.
Wani Bafalasdine a kusa da Masallacin da aka tarwatsa dauke da wasu da kayansa da ya tsira da su a gidansa a Khuzaa da ke kudancin Zirin Gaza. Reuters

Akalla mutane 10 aka kashe a wani hari da aka sake kai wa a wata Makaranta ta Majalisar Dinkin Duniya da mutanen Gaza suka fake saboda hare haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa a yankin.

Talla

An kai harin ne a makarantar da ke kudancin birnin Rafah bayan Isra’ila ta yi wa yankin kaca-kaca da hare hare, sakamakon sace wani Sojanta da aka bayyana ya mutu.

Jami’an lafiya a Gaza sun ce Falasdinawa sama da 40 aka kashe a yau Lahadi, a yayin da kuma Mayakan Hamas ke ci gaba da cilla rokoki zuwa Isra’ila.

Wannan ne karo na uku cikin kwanaki 10 da ake kai hare hare a Makarantu da ke karkashin kuwalar Majalisar Dinkin Duniya, kuma hari mafi muni shi ne harin da Isra’ila ta kai a arewacin garin Jabaliya inda aka kashe mutane 16.

An shafe yanzu tsawon kwanaki 27 Isra’ila na kai hare hare a Gaza, inda aka kashe Falasdinawa 1,766 tare da raunata 9,320.

Isra’ila tace tana kai hari ne domin tarwatsa hanyoyin da Hamas ke harba ma ta rokoki ta karkashin kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI