Ukraine-Rasha

Ukraine tace ta yi nasarar lalata motocin yaki masu sulken kasar Rasha...

REUTERS/Valentyn Ogirenko

Kasar Ukraine ta ce ta lalata wani ayarin motoci masu sulken sojan kasar Rasha, da a jiya juma’a suka kutsa kai a cikin kasarta, a yayin da anata bangaren kasar Amruka ta nemi kasar Rasha da ta daina tsokanar fadan da ta ke yi

Talla

Kakkakin majalisar tsaron shugaban kasar Amruka Barak Obama Caitlin Hayden a cikin wata sanarwa a jiya juma’a ya bayyana cewa a yan makwanin nan kasar rasha ta kara yawaita tsokanar da take yi a kan kasar Ukraine al’amarin da yace kuma yana da matukar hadarin gaske

Mahawara dai ta dada yin zafi ne a yan kwanakin nan tsakanin kasashen turai Amruka, a gefe guda kuma da kasar Rasha.

Tun lokacin da Rasha ta bayyana aniyarta na kai kayayakin jinkai ga jama’ar da yakin da ake tabkawa a yankin Donetsk gabashin Ukrain ya rutsa da su, inda kasashen Turai da Amruka suka nuna rashi amincewarsu da haka, bisa abinda suka kira Rasha na son labewa da agajin ne wajen shigar da makamai ga mayakan aware dake goyon bayanta
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI