Amurka-Iraqi

Mayakan IS na Iraqi barazana ce ga Amurka

Mayaka IS da ke gwagwarmaya a Iraqi
Mayaka IS da ke gwagwarmaya a Iraqi REUTERS/Ibraheem Abu Mustafa

Bangaren tsaron Amurka ya yi gargadin cewa Mayakan IS da ke gwagwarmayar shinfida daular Islama a yanzukunan da suka mamaye a Syria da Iraqi na a matsayin babbar barazanar da Amurka ta fuskanta, tare da shan alwashin kawo karshen ayyukansu.

Talla

Amurka tace ko ana iya kawo karshen ayyukan Mayakan sai idan an samu hadin kan mutanen Iraqi kuma idan sun yi watsi da banbanci akida a tsakaninsu.

Amurka ta yi gargadin cewa Mayakan IS sun wuce abin da aka sani da sauran kungiyoyin ‘yan ta’adda, ta hanyar mallakar makamai, da samun horo a da kudin da suke samu.

A lokacin da ya ke ganawa da manema labaru, Sakataren tsaron Amurkan Chuck Hagel yace barazanar da Mayakan ke yi ya wuce duk abin da aka gani a baya.

Kalaman Hagel na zuwa ne bayan Mayakan na IS sun kashe wani Ba’amurke Jame Foley da ke aikin Jarida a Iraqi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI