IS-Amurka

Mayakan IS sun sake fille kan Ba’amurke

Hoton Bidiyon da Mayakan IS suka kashe Dan Jarida Steven Sotloff.
Hoton Bidiyon da Mayakan IS suka kashe Dan Jarida Steven Sotloff. REUTERS/Social Media Website via REUTERS TV

Kasar Amurka ta ce yanzu haka tana kan gudanar da bincike domin tantance faifan bidiyon da kungiyar IS ta watsa, da ke nuna yadda wani ya fille kan Dan Jarida Steven Sotloff, na biyu da ke hannun mayakan kungiyar.

Talla

A cikin faifan bidiyon mai taken ‘’Sako na biyu zuwa ga kasar Amurka’’ kungiyar ta nuna Steven Sotloff dan shekaru 31 a duniya gurfane akan guwawunsa sanye da wata riga mai launin ruwan goro, yayin da a gefensa akwai wani mutum da ya rufe fuskarsa a cikin bakaken kaya yana rike da wata zungureriyar wuka a hannunsa.

A cikin wannan faifan, barden na kungiyar mayakan Jihadin, ya yi kakkausa suka ga kasar Amurka, kafin daga bisani ya furta kalaman barazanar kashe wani dan kasar Birtaniya da ke tsare a hannun kungiyar mai da’awar kafa daular Musulunci.

Mai Magana da yawun ma’aikatar wajen Amurka Jen Psaki, ta bayyana sakon a matsayin wanda ya girgiza Amurka, sannan kuma ta ce yanzu haka suna gudanar da bincike domin tantance ingancin faifan bidiyon.

Firaministan Birtaniya David Cameron, ya bayyana cewa zai yi iyakacin kokarinsa domin ganin ceto dan kasar da kungiyar ta ISIS ta yi barazanar kashewa a cikin wannan faifan da ta fitar a jiya talata.

A watan Jiya Mayakan sun kashe dan Jarida James Foley a sakon bidiyo na farko da suka aiko.

Kasashen duniya da dama ne dai suka yi Allah waddai da hoton bidiyon da ya nuna yadda aka kashe ‘Yan jaridar. Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi kira ga shugabannin addinai a duniya su tashi tsaye bayan ya yi Allah wadai da kisan Dan Jaridar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.