Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dunkin Duniya na samun koma-baya, ga rage mutuwar Yara kanana.

En Centrafrique, Abigaël, 5 mois, pèse le tiers du poids qu'il aurait normalement dû peser.
En Centrafrique, Abigaël, 5 mois, pèse le tiers du poids qu'il aurait normalement dû peser. RFI

Wani bincike ya nuna cewar yunkurin Majalisar dunkin Duniya na rage mutuwar kananan yara na samun koma-baya sakamakon rashin daukar matakan magance cututtuka masu yaduwa da kuma matsalolin da ake samu wajen goyon ciki da haihuwa

Talla

A karkashin kudurin Majalisar dunkin Duniya na cimma muradun karni, an bukaci daukacin kasashen duniya su rage mutuwar kananan yara da akalla biyu bisa uku daga shekarar 1990 zuwa 2015.

Rahoton ya ce a shekarar 2013 yara sama da miliyan 6 ne suka mutu sabanin kusan miliyan 13 da ake samu a shekarar 1990.

Binciken da Cibiyar kula da lafiya da ke Baltimore, wato School of Public Health, ta gudanar, ya nuna cewar an samu mutuwar yara kananan ne a kasashen China, da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo, da Indiya, da Nigeria da kuma kasar Pakistan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.