Brazil

kiran Marina Silva zuwa mutanen Brazil

Marina Silva,yar takara kuma mai adawa da Shugabar Brazil  Dilma Roussef
Marina Silva,yar takara kuma mai adawa da Shugabar Brazil Dilma Roussef REUTERS/Nacho Doce

‘Yar takarar da ta zo ta uku a zaben shugabancin kasar Brazil da aka gudanar ranar lahadi da ta gabata Marina Silva, ta bukaci magoya bayanta da su jeffa wa abokin karawar shugaba mai ci Aecio Neves kuri’unsu a zaben da za’a gudanar ranar 26 ga wannan wata na Okotoba.

Talla

Marina yar takara da  ta samu fiye da kashi 20 cikin dari a zagayen farko na zaben Brazil, ta bayana adawar ta  da manufofin shugaban mai ci wato Uwargida Dilma Roussef saboda haka take neman akayar da ita a zaben.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.