Algeria

Wani alkalin kasar Fransa ya fara binciken kisan wasu yan addinin Budda a Aljeriya

Lamaman  da aka kashe a Algeria
Lamaman da aka kashe a Algeria

Alkalin kasar Fransa Marc Trevidic a yau lahadi ya ziyarci birnin Alje na kasar Algeria domin binciken kisan da aka yiwa wasu limaman Tibeti  a kasar a 1996

Talla

Ziyarar tasa dai zata dauke shi ne tsawon mako guda a karkashin binciken kisan limaman  yan Tibeti  a kasar ta Algeria a shekarar  1996 

Da farko dai sau biyu yana shirya kai wannan ziyara a cikin watan maris da ya gabata amma mahukumtan kasar ta Algeria suka hana

Su dai mahukumtan Algeria sun bayyana cewa, limaman Buddan faransawa yan asalin yankin Tibeti na kasar China,  kungiyar nan mai zafin kishin addinin islama ta GIA a kasar ta Algeriya ce ta kashe su, amma kuma wasu masu hankoron kare hakkin dan adam sun bayyana cewa, bisa duk alamun da aka samu sun tabbatar da cewa, kisan irin na dakarun  rundunar sojan kasar ta Aljeriya ne, duk kuwa da cewa a wancan lokacin kungiyar ta GIA ta dauki alhakin kisan limaman ta hanyar yi masu yankan rago
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.