MDD na neman kudin agaji don taimaka wa 'yan kasar Iraqi

Sakatare janar na MDD, Ban Ki Moon
Sakatare janar na MDD, Ban Ki Moon REUTERS/Adrees Latif

Har yanzu ana cigaba da fafatawa da mayaka m asu neman kafa daular musulunci, inda suke neman karbe garin Kobane, dake kan iyakar Iraqi da Syria. Jiragen yakin Amurka dana kawayenta sun kashe akalla a kalla 500, a hare-hare da suke kaiwa ta sama da bama-bamai samada 1,700.A ahalin da ake ciki MDD ta kaddamar da wani asusun tallafi samada Dalar Amurka biliyan biyu, don sake raya al’ummar kasar ta Iraqi.Mukaddashin jami’i mai kula da bayar da ajagi na Majalisar ta Dinkin Duniya Neill Wright, yace bukatun al’ummar Iraqi suna da yawa, don haka akwai bukatar samar da kudaden.Wani rahotion MDD ya kiyasta cewa kusan mutane miliyon 3 ne ke bukatar agaji a kasar, yayinda kusan miliyon 1 ke bukatar muhalli cikin gaggawa.Daruruwan mutanen da suka tsere wa tashe tashen hankulan da ake yi a kasar, sun sami mafaka ne a yankin Kurdistan, kuma tsananin sanyin hukuturu zai iya musu illa, a yankin mai tarin tsaunuka.Kwalliya bata biya kudin sabulu ba a baya, lokacin da aka nemi agaji don tallafa mutane da yaki ya raba su da gidajensu a Iraq da makwabciyarta Syria.