Zakuna suna fuskantar barazana a kasashen duniya

Wani nau'in zakin kasar Indiya
Wani nau'in zakin kasar Indiya Open access/Nikunj vasoya

Gwamnatin kasar Amurka tace rashin matsuguni da kuma yadda ake farautar namun daji babbar barazana ce ga rayuwar zakuna a Nahiyar Afrika, tare da cewa zakunan suna bukatar kariya don tabbatuwarsu a doron kasa. Wannan gargadin ya fito ne daga wata cibiyar kula da rayuwar namun dawa da na ruwa a kasar Amurka.Wata sanarwar da cibiyar ta fitar tace rayuwar zakuna na cikin hadarin gaske a nahiyar Afrika, tare da neman gwamnati ta kafa doka akai.Kuma a tsarin dokar, mahukuntan Amurka zasu dauki matakai na tsaurara huldar cinikaiyayya tsakaninsu da kasashen da ake kuntatawa Zakuna.An dai bayyana cewa Zakuna na rayuwa ne ba tare da muhalli ba, saboda yadda ake farautarsu a Nahiyar Afrika. Haka kuma irin nau’in namun dajin da zakuna ke farauta sun fara karewa saboda yawan farautar namun dajin da mutane ke yiCibiyar kula da namun dawan ta Amurka tace wannan ne yasa zakunan ke kashe namun gida, wanda kuma ke sa mutane na daukar fansa, ta hanyar kisan zakunan.Yanzu haka an ba mutanen duniya damar tabka muhawara game da daukar matakai akan kariyar rayukan zakuna a Afrika daga nan har zuwa watanni uku.