Ebola

Faransa zata bayar da tallafin kudi don Ebola

Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola.
Jami'an kiwon lafiya na yaki da cutar Ebola. Reuter

Kasar Faransa tace zata bayar da gudummawar euro miliyan 20 don yaki da cutar Ebola a Nahiyar Afrika, tare da kuma bude wasu cibiyoyin kula da lafiya. Shugaba Francois Hollande ya sanar da shirin wanda ya kunshi gina asibiti mai cin gadaje 200 a kasar Guinea.

Talla

Jami’in kula da yaki da cutar ebola a kasar Jean-Francosi Delfraissy yace nan da kwanaki 10 Faransa zata fitar da kudin.

Tuni dai Shugaban Amurka da kungiyar agaji ta Red Cross suka ce ana samun nasara a yakin da ake yi da Ebola a kasashen duniya.

Hukumar lafiya ta duniya tace a cikin makon nan ne zata fara gwajin rigakafin cutar Ebola a kasar Switzerland.

WHO tace kafin karshen shekara ta 2015 za’a samu wadatuwar dubban rigakafin cutar Ebola mai yin kisa cikin hanzari a kasashen yammacin Afrika. Hukumar tace za’a samar da rigakafin ne kusan Miliyan guda.

Wannan na zuwa ne a yayin da shugabannin kasashen kungiyar Tarayyar Turai suka amince da tallafin kudi sama da euro Biliyan guda domin yaki da cutar Ebola a kasashen Afrika.

Mutane kusan 5,000 suka mutu a kasashen Guinea da Liberia da Saliyo saboda Ebola, kuma masana yanzu sun bayyana fargaba akan barazanar yaduwar Cutar Ebola a kasashen yammacin Afrika.

A cikin makon nan ne aka samu bullar Cutar Ebola a Mali bayan cutar ta bulla a Najeriya.

Kimanin mutane 43 ne ake lura da lafiyarsu a Mali wadanda suka yi mu’amula da wata yarinya ‘Yar shekaru biyu da ta yi sanadin bullar cutar Ebola a cikin kasar daga Guinea.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.