Hukumar lafiya ta duniya fitar ka'idojin anfani da makamashi a cikin dakuna
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Hukumar lafiya ta Duniya ta bayar da sanarwar samar da ka’idojin amfani da makamashi a cikin dakuna. Wannan shine karin farko da hukumar ta taba fidda irin wadannan ka’idojin, don kare lafiyar jama’a.Ana fatan ka’idojin zasu taimaka wajen rage yawan mutanen dake mutuwa, sakamakon hayakin makamashin da ake amfani da shi a cikin dakuna.Hukumar ta gano cewa a kalla mutane miliyon 4 ne ke mutuwa sakamakon yadda ake amfani da makamashi don dumama dakuna, girki, da ma fitilun aci bal bal.Kona makamashi kamar Coal da ba a sarrafa shi ba, da Kalanzir a cikin dakuna, na matsayin abu na farko dake gurbata dakuna.Matsalar tafi tsanata a kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu, sakamakon yadda mutane basa iya amfani da makamashi na zamani Hukumar lafiyan tace kusan mutane miliyon dubu 3, wato kusan rabin al’ummar duniya basu da yadda zasu sami tsaftattaccen makamashi, don girki dumamawa da haskaka dakuna ba tare da shiga hadari ba.Don haka ta nemi hukumomi a kasashe su fadada yadda za a samar da makamashi da baya tattare da hadari, ko kuma a wadata al’ummomi da wutar lantarki.