Yau ake bukin ranar yaki da cutar AIDs ko SIDA a duniya

Wajen taron yaki da cutar SIDA da aka yi a birnin Melbourne na kasar Australiya
Wajen taron yaki da cutar SIDA da aka yi a birnin Melbourne na kasar Australiya International AIDS Society/Steve Forrest

Majalisar dinkin duniya ta ware yau 1 ga watan disamba, a matsayin ranar yaki da cutar SIDA wato AIDS ta duniya. Wannan rana ce da ake maida hankali wajen wayar da kanun jama’a kan abubuwa dake haddasa yaduwar cutar ta SIDA.A sakonsa na bana, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, yayi kira da’a kawo karshen banbance-banbance tsakanin al’umma, musamma ta hanyar rage kyamatar masu dauke da cutar, a matsayin hanyar kawo karshan cutar a duniya, kafin shekarar ta 2030.Tun cikin shekarar ta 2004 Majalisar ta Dinkin Duniya tare da haddin gwiwa hukumar lafiya ta duniya WHO, suke gudanar da bukukuwan wanna ranar, tare da jan hankalin gwamnatoci, hukumomi, da kungiyoyi masu zaman kansu dama daidaikun mutane, don ganin an hadda karfi da karfe don ilimantar da jama’a akan cutar ta SIDA da kuma yadda za a takaita yaduwar cutar tsakanin alumomiA kowace shekara, ranar kan zo da taken ta, a bana bijiro da sababbin hanyoyin kariya da rigakafi shine abinda ranar ta mai da hankali a kai, inda ake cewa a yanzu ana samun raguwa wajen yaduwar wanna cutarA jawabinsa na bana Sakatar Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon, ya yi kira ga shugabani al’umomi dasu hadda hannu wajen kawo karshen cutar kafin shekarar ta 2030.Ban yace samar da sauyi musamma ta fanin zamanatakewa tsakanin al’ummah, ta hanayar daidaito da rashin nuna kyamata tsakanin al’umma, na matsayin babban makami na kawo karshen cutar.A shekarara data gabata, cutar ta SIDA tayi sanadiyyara mutuwar sama da mutane miliyan 36, yayin da wasu fiye da miliyon 35 ke fama da cutar a duniya.