Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dunkin Duniya ta bukaci a yi adalci ga masu zanga-zanga a Amurka

cleveland.com

Majalisar dunkin Duniya ta bukaci kasar Amurka da ta duba yanayin aikin jami’an ‘yan sandan kasar, bayan da aka kasa daukar mataki, duk da jerin zanga-zangar da aka yi, sakamakon harbin da wani dansanda farar fata ya yiwa wani bakar fata farar Hula da baya rike da makami wato Eric Garner a kasar, kuma ya mutu

Talla

An ce dai a maimakon daukar matakin sasanta lamarin daga bangaren hukumomin kasar ta Amurka, jami’an ‘yan sandan kasar sun kama mutane da dama masu zan-zanga a biranen kasar daban daban.

Masu zanga-zangar dai na neman lallai hukumomin kasar at Amurka su dauki mataki akan wannan jami’in dansanda da ya yi kisan Eric Garner da mai magana da yawun Majalisar dunkin Duniya Stephene Dujarric ke cewar babu adalci a ciki.

Kasar Amurka dai na kan gaba-gaba cikin kasashen da ke kurarin kare ‘yancin bil’adama a Duniya, amma wannan al’amarin, ya haifar da yadda al’ummar Duniya ke mata kallon Macijiyar Soshiya.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.