Kotun Afrika ta kudu ta wanke Dewani
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Kotun kasar Afrika ta kudu ta wanke attajirin kasar Birtaniya Shrien Dewani da laifin kisan Amaryar shi da gangan a lokacin da suka je shakatawa bayan aurensu. Mai shari’ar Diwani, ta yi watsi da hujjojin da masu shigar da kara suka gabatar.
Masu shigar da karan sun bayyana cewa, Dewani ya yi hayar a kashe matarsa ne ta hanyar bugu, sakamakon cewa, danginsa sun masa auran dole da matar, al-amarin da ya sa shi fusata, kasancewar shi mai neman maza ne.
A watan Nuwamban shekara ta 2010 ne aka kashe Amaryar ta Dewani birnin Cape Town. Kuma Dewani ya musanta zargin da ake ma sa, inda ya bayyana cewa, tabbas shi mai neman maza ne da mata amma duk da haka, yana kaunar matarsa.
Kubutar Dewani daga hannun kotu ta haifar da karamar zanga zanga, a harabar kotun, inda jama’a ke cewa, ba a yi hukuncin bisa adalci ba, saboda Dewani attajirin mai kudi ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu