Canada-IS

Musulmin Canada sun yi tir da kalaman mutumin da ya musulunta

Dan kasar Canada John Maguire da ya yi kiran a kaddamar da hari a kasar bayan ya karbi musulunci a hannun Mayakan IS
Dan kasar Canada John Maguire da ya yi kiran a kaddamar da hari a kasar bayan ya karbi musulunci a hannun Mayakan IS Youtube grab via al arabiya

Al’ummar Musulmin kasar Canada sun yi Allah wadai da kiran da wani Dan kasar ya yi na kaddamar da hare hare a cikin kasar jim kadan bayan ya karbi addinin Islama daga hannun Mayakan IS da ke da’awar Jihadi a Iraqi da Syria. Majalisar Musulmin kasar sun nesanta kansu kamar yadda kakakinsu Imam Sikander Hashmi ya bayyana.

Talla

Akwai ‘Yan kasar Canada biyu da Mayakan IS da ke da’awar Jihadi suka kashe.

Imam Hasmi ya ce duk wani yunkuri na kai hari kan jama’ar da ba su ji ba su gani ba, ya sabawa addinin Islama.

A cikin wanin sakon bidiyon, Dan kasar ta Canada mai suna John Maguire, yace Canada zata fuskanci sabbin hare hare a matsayin martani ga kawancen da ta kulla da Amurka na kai wa Mayakan IS hari ta Jiragen sama.

Baturen na Canada ya sauya sunansa zuwa Anwar al Canadi bayan ya karbi musulunci tare da kira ga musulmi su fara kisan makiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.