Isra'ila

An sake zabar Netanyahu a matsayin shugaban Jam’iyya mai mulki

Firaministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila, Benyamin Netanyahu REUTERS/Amir Cohen

An sake zabar Fraiministan kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu, a matsayin shugaban jam’iyyar Likud mai mulkin kasar, a wani zaben fitar da gwanin da aka yi jiya Alhamis. Zaben na zuwa ne a daidai lokacin da ake shirin yin wani zaben gaggawa a kasar, inda ya kayar da abokin takarar shi Danny Danon mai ra’ayin gurguzu.

Talla

Natanyahu da ke rike da madafun ikon kasar tun shekarar 2009, na fatan zarcewa a karo na 3 a jere, kuma karo na 4 gaba daya, bayan da ya taba jagorantar kasar tsakanin shekarar 1996 da 1999.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.