Libya

Al Libi na Libya ya rasu kafin soma shari’arsa a Amurka

Abu Anas Ali Libi na Libya
Abu Anas Ali Libi na Libya France24

Dan kasar Libya da ake zargi da hannu ga harin da Mayakan Al Qaeda suka kai wa ofishin jekadancin Amurka a wasu kasashen Afrika ya rasu kafin a fara gudanar da shari’arsa a birnin New York. Lauyan da ke kare Abu Anas al Libi da iyalansa ne suka tabbatar da mutuwarsa a wata asibitin birnin New York a jiya Juma’a.

Talla

A ranar 12 ga Janairu ne al Libi zai gurfana gaban kotu kan zargin kaddamar da hare hare a ofishin jekadancin Amurka a Kenya da Tanzania inda mutane 244 suka mutu tare da raunata sama da 5,000.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.