Amurka

Gambia: Amurka na tuhumar mutane biyu da laifin juyin mulki

Shugaban kasar  Gambia Yahyah Jammeh
Shugaban kasar Gambia Yahyah Jammeh AFP PHOTO/Don Emmert

Masu shigar da kara a kasar Amurka suna tuhumar wasu mutanen kasar Gambia da laifin yunkurin hambarar da gwamnatin Yahya Jammeh a wani yunkurin juyin mulki da aka murkushe a makon da ya gabata.

Talla

Jami’an tsaron Amurka sun cafke mutanen biyu ne ‘yan asalin kasar Gambia kuma Amurkawa bayan sun dawo daga Gambia inda ake zargin sun tafi kasar ne domin kitsa juyin mulkin da aka murkushe a ranar 30 ga watan Disemba.

Bangaren shari’ar Amurka ya bayyana sunayen mutanen a matsayin Papa Faal da Cherno Njie mazauna Amurka

Faal mai shekaru 46 zai gurfana gaban kotun Amurka a jihar da ya ke zama Minnesota, yayin da kuma Cherno Njie zai gurfana a gaban kotun Texas a ranar yau Litinin.

A cikin wata sanarwa Alkalin alkalai Eric Holder ya fadi cewa mutanen biyu sun sabawa dokokin Amurka akan tafiya kifar da wata gwamnatin kasar waje.

A lokacin da Faal ke amsa tambayoyi ya amsa cewa yana cikin gungun mutanen da suka yi yunkurin juyin mulki a Gambia tare da danganta Cherno Njie a matsayin wanda ya jagoranci juyin mulki da nufin darewa saman mulki idan sun cim ma nasara.

Yahaya Jammeh dai ya kwashe tsawon shekaeru 20 yana shugabanci a Gambia kuma an yi yunkurin kifar da gwamnatinsa ne a lokacin da ya ke ziyara a Dubai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.