Syria

Mutanen Syria 704,000 suka yi gudun hijira a watanni shida

Mutanen Syria da ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Lebanon
Mutanen Syria da ke kokarin tsallakawa zuwa kasar Lebanon REUTERS/Hassan Abdallah

Majalisar Dinkin Duniya ta ce adadin ‘yan gudun hijirar kasar Syria ya ta shi zuwa 704,000 a cikin watanni shida kacal, kuma a yanzu haka sune mafiya yawa da Majalisar ke kula da su. Wannan na zuwa ne bayan UNICEF tace yara 160 aka kashe bara yayin da kusan miliyan biyu da rabi ke fuskantar barazanar rashin samun ilimi.

Talla

Rahotan na cewa a cikin shekarar ta 2014 da ta gabata an kai jerin hare-hare a makarantu sama da 68 a Syria, wanda ya yi sanadin mutuwar dalibai da jikata da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.