Faransa

Musulmin kasar Faransa sun nisanta kansu ga harin Hebdo

rfi

Kungiyoyin musulmi da dama daga kasar Faransa, sun bayyana bacin ransu da harin da aka kaiwa Mujallar Charlie Hebdo, wadda a baya ta wallafa zanen batanci ga fiyayyen halitta Muhammad [saw]

Talla

Yanzu haka dai Kungiyoyin musulmin sun yi kira ga al’ummar Musulmin daga sassan kasar da daban daban da su yi shiru na dan lokaci, domin nuna alhininsu ga harin.

Kungiyoyin musulmin haka ma sun bukaci Imamai a dukkanin Masallatan Jumu’a a kasar Faransa da ma Duniya baki daya, da su gudanar da Hudubobi da addu’o’I na musamman domin samar da kariga masu neman bata sunan musulunci bisa wasu akidu.

Yanzu hada dai Jami’an tsaron kasar ta Faransa na aiki wurjanjan domin zakalo wadanda suka kai harin na Charlie Hebdo, a yayin da ake ci gaba da zaman makoki a dukkanin fadin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.