Faransa

Al Qaeda ta yi barazanar kai wa Faransa hare hare

Wata Mata tana rike da mujallar Charlie da ta ci zarafin Musulmi
Wata Mata tana rike da mujallar Charlie da ta ci zarafin Musulmi REUTERS/Michael Dalder

Kungiyar Al Qaeda da ke Arewacin Afrika ta gargadi kasar Faransa cewar zata ci gaba da kai wa kasar hari kan yadda ta ke nuna adawa ga addinin islama, inda ta yabawa maharan da suka kai hare haren makon jiya. Kamfanin Dillancin labaran Faransa ya ruwaito wata sanarwa da kungiyar ta sanya a shafin ta inda tace Faransa na biyan diyyar yadda take musgunawa al’ummar Musulmi da kuma yadda ta ke matsawa addinin.

Talla

Kungiyar tace muddin kasar za ta ci gaba da girke sojojinta a Mali da Afrika ta Tsakiya da kuma kai hare hare a Syria da Iraqi, da kuma yadda kafofin yada labaran kasar ke cin zarafin Manzon Allah Fiyayyen Halitta SAW, kasar za ta fuskanci fushin kungiyar.

Amma a lokacin da ya ke jawabin a bikin karrama wadanda aka kashe a harin Charlie Hebdo, Shugaban Faransa francois Hollande yace za su ci gaba da yaki da ta’addanci.

A makon jiya ne wasu mahara suka kashe ma’aikatan Mujallar Charlie 12 a matsayin martani ga cin zarafin Musulmi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.