Faransa

Mujallar Charlie ba ta daddara ba

Shagon sayar da Jaridu a Paris
Shagon sayar da Jaridu a Paris rfi

Mujallar Charlie Hebdo da ake bugawa a mako a Faransa ta sake wallafa wani zanen mutum da ta danganta da Annabi Muhammad SAW a shafinta na farko da ta fitar a wannan makon, duk da ma’aikatanta 12 da aka kashe a harin da aka kai wa Ofishinta.

Talla

Editan mujallar Gerard Biard yace kwafin mujallar miliyan uku aka buga a harsuna da dama domin sayarwa mako guda bayan harin da wasu yan bindiga suka kai ginin majullar.

Wannan na zuwa ne a yayin da Gwamnatin Faransa ta kara baza sojoji domin inganta tsaro a cikin kasar.

Mujallar ta buga kwafi ne mai dauke da zanen Mutum yana rike da alamar rubutun “ Ni Charlie ne” da kuma wani rubutun “ Mun yafe komi”.

Da safiyar Laraba an sayar da kwafin Mujallar da ta fara rabawa, yayin da al'ummar Musulmi ke yin allawadai da mujallar da wadanda ke ra'ayin sake wallafa zanen daidai ne.

A makon jiya ne wasu mahara guda biyu da aka bayyana ‘yan uwan juna suka kaddamar da hari a ofishin Mujallar inda suka kashe yan Jarida 12. Maharan sun kai wa Mujallar hari ne domin mayar da martani ga zanen da ta yi a 2011 da ya ci zarafin musulmi.

Jimillar mutane 17 aka kashe a cikin kwanaki uku a hare haren da ‘Yan bindiga suka kaddamar a birnin Paris.

Kimanin mutane Miliyan hudu ne suka shiga gangamin nuna alhini ga harin da aka kai wa Mujallar Charlie Hebdo a ranar bakwai ga watan Janairu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.