Amurka-Iran

Power ta gargadi Amurka akan Iran

Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power
Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power REUTERS/Eduardo Munoz

Jekadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Samantha Power ta yi gargadi ga Majalisar kasar akan karfafawa kasar Iran takunkumi zai iya kawo cikas ga tattaunawar nukiliya tsakanin Iran da manyan kasashen duniya.

Talla

Jekadiyar ta Amurka tace karfafawa Iran takunkumi na iya kawo karshen tattaunawar nukiliya da manyan kasashen duniya ke yi da kasar.

A cewarta kakabawa Iran sabbin takunkumi matsala ce ga yarjejeniyar da suke kokarin amincewa da Iran akan dakatar da shirinta na Nukiliya.

Wannan gargadin kuma na zuwa ne kafin wata ganawa da za a yi tsakanin Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry da ministan harakokin wajen Iran Javad Zarif a Geneva a ranar Laraba inda ake fatar bangarorin biyu za su shata hanyoyin da za a samu maslaha da Iran.

Iran dai na tattaunawa ne da Amurka da Birtaniya da Faransa da Rasha da kuma Jamus wadanda ke son cim ma yarjejeniya da ita a karshen watan Yuni bayan sun kasa samun jituwa a lokaci mai tsawo da suka kwashe suna tattaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.