Faransa

Al Qaeda ce ta kai wa Mujallar Charlie hari

Shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman Zawahiri
Shugaban Kungiyar Al Qaeda Ayman Zawahiri REUTERS/Social Media Website via Reuters TV

Kungiyar Al Qaeda a reshen Yemen tace ita ce ta kai wa Muallar Charlie Hebdo hari a Faransa a cikin wani sakon bidiyo da kungiuar ta sa a Intanet. Kungiyar tace martani ne akan Mujallar saboda da zanen da ta danganta da Manzon Allah SAW. Kwamandan Kungiyar Nasser al Ansi yace Shugaban Kungiyr Al Qaeda ne Ayman al Zawahiri ya bayar da umurnin a kai wa Mujallar hari.

Talla

Nasser ya ce an zabi jarumai ne domin su aiwatar da harin akan makiya Manzon Allah tare da yin gargadi ga kasashen yammaci su shiga taitayinsu ga fakewa da 'yancin tofa albarkacin baki suna nuna kiyayya ga Musulmi

Kwamandan na Al qaeda da ya fito a Bidiyon yace idan babu iyaka ga ‘yancin tofa albarkacin baki, ya zama wajibi ga kasashen Turai su amince da hare haren da suke kai wa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.