Faransa

An bukaci Musulmi su kwantar da hankalinsu

Jami'an tsaro suna gadin Masallacin a Paris
Jami'an tsaro suna gadin Masallacin a Paris REUTERS/Youssef Boudlal

Kungiyoyin alummar musulmi a kasar Faransa sun nemi musulmi da su kwantar da hankulansu sakamakon sabon zanen da Mujallar Charlie Hebdo ta wallafa da ke kara yin wani batanci ga addinin Islama.

Talla

Wannan kiran da kungiyar ta yi na kunshe ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a jiya Talata inda suka bukaci hadin kan musulmai na yankin da su dauke ido daga duk wani sakon da Mujjalar ta fitar.

Lauyan Mujallar ta Charlie Hebdo ya kare matakin cewa Faransa kasa ce da ke da ‘yancin bayyana ra’a yi kuma koda ra’ayin ya sabawa addinai.

Amma duk da wadannan kalaman Kungiyar Musulmi a Faransa ta bukaci mabiya addinin su kwantar da hankulansu tare da gujewa duk wani al’amari da zai tunzura su wajen mayar da martani

A ranar Larabar da ta gabata ne dai wasu 'yan ‘Yan bindiga suka kai hari a ofishin mujallar ta Charlie Hebdo harin da ya haddasa hasarar rayukan mutane 12 .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.