Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar dinkin Duniya ta bukaci daidaito kan jinsi a Duniya

zwallpix.com

Majalisar Dinkin Duniya ta bude wani taron daidaita jinsi inda a bana ta bayar da fifiko akan baiwa mata yanci kamar yadda maza ke dashi acikin al’umma

Talla

Taron wanda kasar Iceland ta shirya ya samu halartar wakilai na wasu kasashe da kuma jami’ai na Majalisar Dinkin Duniya inda za’a shiga tattaunawa akan matakan da maza yakamata su dauka na dakatar da cin zarafin mata.

Kasar Iceland wacce ta kasance kasa a nahiyar Africa da mace ke shugabanta ta bukaci bawa mata dama a taron.

Taron dai na fatar kafa wata sabuwar fage da zai bawa duk jinsi damar bayyana ra’ayi
A cigaban taro na bana ana sa ran wakilan zasu dauki alkawarin tursasa.

Gwamnatocinsu wajen shiga mahawarar da zai bawa mata damar samun yanci kamar maza.

Wannan taron dai na zuwa ne a daidai lokacin da MDD ke shirin bikin cika shekaru 20 da taron mata na Beijing taron da ya mayar da hankali akan kawo karshen wariyar jinsi da taron ya yi kokarin ganin an kawo karshensa baki daya a shekara ta 2030.

Kasar Iceland itace kasar da aka fi samun tazarar yanci tsakanin mata da maza yayin da kasar Yemen ke ta 142 a jerin kasashen duniya da mata basu da tacewa.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.