Faransa-Afrika ta Tsakiya

An sace wata Bafaransa a Afrika ta tsakiya

Bangui babban birnin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya
Bangui babban birnin kasar Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya AFP PHOTO / PACOME PABANDJI

Fadar Shugaban Kasar Faransa ta sanar da cewa wasu ‘Yan bindiga sun sace wata ‘Yar kasar mai shekaru 67 da ke aikin agaji a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Faransa ta yi allawadai da matakin inda ta bukaci wadanda suka sace Baturiyar su gaggauta sakinta cikin gaggawa. Bayani sun ce yanzu haka ofishin Jakadancin Faransa da ke Bangui na tattaunawa da shugaban kiristocin birnin domin tuntubar a wadanda suka sace matar.

Talla

Ana dai zargin Mayakan anti balaka ne suka sace jami'ar agajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.