Hague

Kwamandan ‘Yan tawayen Uganda ya isa kurkukun ICC

Hoton Kwamandan 'Yan yawayen Uganda Dominic Ongwen a wata jaridar kasar.
Hoton Kwamandan 'Yan yawayen Uganda Dominic Ongwen a wata jaridar kasar. AFP PHOTO / ISAAC KASAMANI

Kwamandan ‘Yan tawayen Lord’s Resistance Army na Uganda ya isa kurkugun kotun hukunta manyan laifukan yaki ta ICC a birnin Hague domin fuskantar shari’ar zargin  laifukan yaki da cin zarafin Bil adama da ya aikata a kasashen da ke tsakiyar Afrika. Kakakin Kotun Fadi El Abdallah ya shaidawa Kamfanin dillacin labaran Faransa cewa sun karbi dominic Ongwen a birnin Hague wanda ya mika kansa ga dakarun Amurka a Jamhuriyar tsakiyar Afrika.

Talla

Ongwen yana cikin shugaban ‘Yan yawayen Uganda wadanda ake zargi da kisan mutane sama da 100,00 a ta’adin da suka fara a 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.