Hague

Kwamandan ‘Yan tawayen Uganda a Kotun ICC

Kwamandan 'Yan tawayen Uganda Ongwen
Kwamandan 'Yan tawayen Uganda Ongwen Reuters

Kotun duniya ta ICC a birnin Hague zata fara Shari’ar Daniel Ongwen Kwamandan ‘Yan tawayen Lord's Resistance Army na Uganda a yau Litinin wanda ake zargi da aikata laifukan yaki da suka shafi kisa da bautar da yara kanana.

Talla

A makon jiya ne dakarun Afrika a Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya suka mika Ongwen ga kotun ICC bayan ya mika kansa ga dakarun Amurka.

Shari’arsa ita ce ta farko da wani mamban ‘Yan tawayen Uganda ya gurfana a kotun ICC.

Ongwen yana cikin shugabannin ‘Yan yawayen Uganda wadanda ake zargi da kisan mutane sama da 100,00 a ta’adin da suka fara a kasashen tsakiyar Afrika a 1987.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.