Syria

‘Yan adawar Syria na tattaunawa a Moscow

Shugaban Syria, Bashar al-Assad yana ganawa da wakilan kasar Algeria
Shugaban Syria, Bashar al-Assad yana ganawa da wakilan kasar Algeria REUTERS/SANA/Handout via Reuters

Shugabannin ‘Yan adawar Syria da ke fada da gwamnarin Bashar al Assad sun fara ganawa ta kwanaki hudu domin tattautana yadda za a kawo karshen rikicin kasar na tsawon shekaru hudu, da aka kashe dubban mutane. Ana sa ran Shugaban Syria Bashar Al Assad ya turo da wakilai a zaman tattaunawar da Rasha ke jagornta.

Talla

‘Yan tawayen sun soma ganawar ne a yau Litinin, kuma ana sa ran za su kammala zuwa ranar Alhamis.

Rahotanni daga Rasha sun ce manyan ‘Yan adawar kimanin 25 ne suka halarci zaman tattaunawar. Sai dai akwai wani bangare na ‘Yan adawar da suka kauracewa taron.

Kasar Rasha da ke nuna goyon bayanta ga gwamnatin Bashar Al Assad tana fatar jagorantar sulhu ne a tsakanin bangarorin biyu, yayin da wani bangaren na ‘Yan adawa ke ganin wata kasa da ba ruwanta ya kamata ace ta jagoranci tattaunawar.

Sama da rayukan mutane 200,000 Majalisar Dinkin Duniya tace aka kashe tun soma rikicin Syria a 2011.  Miliyoyan mutane ne kuma suka tsere daga Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.