Amurka

Komi ya tsaya tsak a New York saboda Iska da Dussar Kankara

Dussar Kankara da ke zuba a kasar Amurka
Dussar Kankara da ke zuba a kasar Amurka REUTERS/Michelle McLoughlin

Iska mai karfi da dussar Kankara da ke zuba ya sa dole an dakatar da zirga-zirgar ababen hawa a birnin New York da arewa maso gabacin Amurka, al’amarin da ya shafi miliyoyan mutanen Amurka. Yanzu haka an soke tashi da saukar jiragen sama kusan 7,000 tun daga ranar Litini saboda matsalar yanayin da ya shafi yankin na arewacin kasar.

Talla

Hukumomin New York sun dakatar da harakokin sufuri, tare da kafa dokar ta-baci a yankunan da matsalar yanayin ta fi kamari.

Mahukuntan Amurka sun yi gargadin cewa za a samu matsalar katsewar wutar lantarki da faduwar itace saboda kadawar iska mai karfi da ke tafe da dussar kankara.

A yau Talata an rufe Makarantu a New York tare da soke jarawaba da dalibai ke shirin rubutawa. Majalisar Dinkin Duniya ma ta rufe babban Ofishinta.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.