Amurka

Yana da wahala a rufe Guantanamo -Hagel

Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel
Sakataren Tsaron Amurka Chuck Hagel REUTERS/Yuri Gripas/files

Tsohon shugaban Gidan Yarin Guantanamo Chuk Hagel, ya ce abu ne mai wuya a rufe gidan Yarin na kasar Amurka a karshen wa’adin shugaba Barack Obama. Hagel a zantawa da wata kafar Radio ya ce yana da wahala a kula da batun sauyawa wasu ‘yan gidan kason na Guantanamo wurin da ake tsaresu daga nan zuwa wasu wurare.

Talla

Shugaba Obama ya ta nanata shirin rufe gidan kason amma ‘yan Majalisar kasar suka yi ta taka ma sa birki.

Musamman lura da kudurinsa na mayar da wasu daga cikin ‘yan gidan kason a kasar Amurka, amma jami’an harkokin Diplomasiyya na kasar ta Amurka na ci gaba da neman kasahen da ke bukatar a kai ma su wadannan ‘yan gidan kaso da kasar Amurka mai ci gaba da rike su bata bukata.

Sai dai akwai alkalumman da ke bayyana cewar sannu a hankali yawan ‘Yan gidan kason na ci gaba da ragewa tun bayan da shugaba Obama ya hau Karagar mulkin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.